Wasu kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya sun yi kira ga gwamnatin Najeriya kan inganta yi wa yara allurar rigakafin cutar sanyi na hakarkari ‘Pneumonia’ domin dakile yaduwar cutar a kasar.
Kwararrun sun yi wannan kira ne a taron sanin makama game da illar yaduwar cutar da kungiyar ‘Save the Children International’ ta shirya a Abuja ranar Litini.
Shugaban kungiyar Ben Foot ya bayyana cewa a kan kamu da cutar sanyi na hakarkari ‘Pneumonia’ a dalilin kamuwa da wasu kwayoyin cututtuka wanda idan ba a gaggauta neman maganin ba sai ya kan yi ajalin mutum.
Cutar hakarkari cuta ce da ta fi kama yara kanana musamman ‘yan kasa da shekara biyar sannan bincike ya nuna cewa a shekaran 2015 cutar ta kashe yara ‘yan kasa da shekara biyar 920,000 a duniya baki daya.
Yace inganta yin allurar rigakafin cutar nan da shekara 15 zai taimaka wajen ceto rayukan yara miliyan 5.3 a duniya.
A dalilin haka Foot yake kira ga gwamnatocin kasashen duniya da su zage damtse don ganin an hana yaduwar wannan cutar.
Bayan haka shugaban kungiyar likitocin Najeriya (NMA) Francis Faduyile ya yi kira ga gwamnatin Najeriya kan tilasta samun inshoran kiwon lafiya wa mutanen kasa Najeriya domin inganta kula a fannin kiwon lafiyar kasar.
A karshe jami’ar gidauniyyar Bill da Melinda Gates, Paulin Basinga da jami’in UNICEF Mohammed Fall a nasu tsokacin sun ce za su mara wa gwamnatin Najeriya baya wajen ganin an inganta bada allurar rigakafin cutar a Najeriya domin ceto rayukan yara kanana.