CIWON SIGA: Za a samu karancin karancin maganin ‘Insulin’ nan da shekarar 2030 – Bincike

0

CIWON SIGA: Za a samu karancin karancin maganin ‘Insulin’ nan da shekarar 2030 – Bincike

Masu bincike daga jami’ar Stanford dake kasar Amurka sun bayyana cewa nan da shekara 2030 duniya za ta yi fama da karancin maganin ciwon siga ‘Insulin’.

Shi Insulin ya na aiki ne a jiki wajen tace sinadarin ‘Carbonhydrate’ dake cikin abincin da muke ci don samar wa mutum kuzarin da yake bukata a jiki.

Rashin aikin ‘Insulin’ yadda ya kamata ne ya ke sa a kamu da ciwon siga.

Masu binciken sun bayyana cewa za a sami wannan matsala ne ganin cewa ana samun karin yawan mutanen da ke dauke da cutar.

An gano haka ne a binciken da suka gudanar a kasashe 221 inda ya nuna cewa masu dauke da cutar siga za su karu daga miliyan 406 a shekaran 2018 zuwa miliyan 511 a 2030 a fadin duniya.

Binciken ya kuma kara nuna cewa idan har gwamnatocin kasashen duniya basu gaggauta daukan mataki ba mutane miliyan 38 daga cikin miliyan 79 ne kawai za su iya samun magani a wannan lokaci.

Idan ba a manta ba a kwanakin bayane wasu ma’aikatan kiwon lafiya suka yi kira ga mutane kula da abobuwan da suke ci da yadda suke tafiyar da rayuwar su domin guje wa kamuwa da cutar siga.

Alamun wannan cutar sun hada da yawan jin kishi, yunwa, yawan yin fitsari, kasala da dai sauran su.

Bincike ya nuna cewa mutane miliyan hudu na dauke da wannan cutar sannan daga cikin su kashi 70 zuwa 80 basu da masaniya cewa suna dauke da cutar. Sannan da dama sun rasa rayukan su a dalilin wannan cutar saboda talauci.

A dalilin haka ministan kiwon lafiya Isaac Adewole da wasu ma’aikatan kiwon lafiya suka yi kira ga kungiyoyin da suka hada kawance da su goya wa kokarin da gwamnatin tarayya ke yi kan kawar da ciwon a Najeriya.

Ma’aikatan kiwon lafiyar sun kuma bayyana wasu alamun hanyoyin gujewa kamuwa da wannan cutar.

Ga hanyoyin:

1. Zuwa asibiti domin yin gwajin wannan cutar don sanin matsayin mutum.

2. A tabbata ana cin abincin dake taimakawa wajen inganta garkuwan jiki kamar su cin ganyayakin da ake ci da kayan lambu.

3. A guji cin abincin dake kawo kiba a jiki kamar su Alawar cakulate, kayan zaki, giya, sigari, gishiri, beredi da sauran su.

4. A rika motsa jiki da guje wa yawan sa kai cikin damuwa.

5. Mata za su iya shayar da ‘ya’yan su ruwan nono kamar na tsawon shekaru biyu domin gujewa kamuwa da wannan cutar.yukkan da za a yi da wadannan kudade.

Share.

game da Author