Bincike ya nuna cewa kashi 20 zuwa 30 daga cikin miliyan 200 na mutanen Najeriya na fama da matsala na tabuwar hankali.
Haka ya nuna cewa a mutane 10, 3 na fama da matsalar tabuwar hankali a kasar nan.
Jami’in ma’aikatar kiwon lafiya Abdulaziz Abdullahi ya bayyana haka a wani taro da aka yi a Abuja.
Abdullahi ya ce a Najeriya matsalolin rikici, aiyukkan Boko Haram da amfani da miyagun kwayoyi na daga cikin ababen dake jefa mutane cikin wannan yanayi da su kan sami kan su.
Wayar da kan mutane game da illolin amfani da mugan kwayoyi, kawar da rikici musamman aiyukkan Boko Haram na cikin matakan da ya kamata gwamnatin kasar nan ta dauka.
Discussion about this post