Buhari ya saka hannu a kudirin dokar kafa hukumar hana yaduwar cututtuka, NCDC

0

A yau Talata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan kudirin dokar kafa hukumar hana yaduwar cututtuka na kasa (NCDC).

Buhari ya yi haka ne bayan hukumar ta yi shekaru bakwai tana aikin hana yaduwar cututtuka a Najeriya.

Shugaban hukumar Chikwe Ikekweazu yayin da yake jinjina wa gwamnatin Buhari kan kafa hukumar bisa doka da ta yi ya bayyana cewa hakan ya nuna yadda wannan gwamnatin ta maida hankali wajen inganta kiwon lafiyar mutanen kasar nan.

Chikwe NCDC

Chikwe NCDC

” Ina tabbatar muku da cewa kafa wannan hukuma da gwamnati ta yi bisa doka zai sa mu zage damte wajen ganin mun dakile yaduwar cututtuka a kasar nan.

Share.

game da Author