Buhari ba abin amincewa ba ne – Atiku

0

Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana dalilan sa na cewa ba za a iya gaskata kalaman Buhari na alwashin da ya dauka ba, cewa zai iya amfani da karin mafi kankantar albashi zuwa naira 30,000.

Cikin wani jawabi da ya fitar, Atiku ya ce idan aka dubi yadda Buhari ke yawan yin kwan-gaba-kwam-baya, to ba shi da kuzari da karfin halin iya zartas da fara biyan karin mafi kankantar albashin, kamar yadda kwamiti ya kai masa rahoto.

Atiku ya ce idan aka yi duba, za a ga cewa ma’aikata sun cancanci karin, domin su ne kashin bayan masu gudanar da aiki da ma tafiyar da shi, yadda wannan gwamnatin ke cin moriyar su.

Atiku ya yi amfani da wannan dama ya kara tunatar da yadda wannan gwamnati ke sakaci da rashin iya gudanar da tattalin arziki, har bankunan kasashen waje irin su HSBS da UBS suka fice daga Najeriya.

Ya kuma ce irin dalilin da bankunan suka bayar na kwashe kayan su daga kasar nan, shi ne dai mashahurin kamfanin nan, Procter and Gamble ya bayar a lokacin da zai daina hulda a cikin Najeriya.

Ya ce kamfanoni 500 sun fice daga kasar nan, daga farkon hawan Buhari zuwa yanzu.

“Mu na sane da cewa Shugaban Kasa da Mataimakin sa su na karbar alawus na kashi 50 bisa 100 na albashin su na shekara, amma kuma sun yi watsi da bukatun kara wa ma’aikata albashi mafi kankanta, domin su dan samu karin abin cefane, su dan gusa daga kuncin da su ke fama da shi na rashin albashi isasshe.”

Share.

game da Author