Boko Haram sun sace shanu 200 da tumakai 300, sun kona gidaje 65 a kauyen Bale-Shuwa

0

Hukumar Kula da Agajin Gaggawa, NEMA, ta ruwaito cewa Boko Haram sun kutsa kai a cikin dare ranar Asabar da ta gabata a kauyen Bale Shuwa, inda suka saci shanu 200 da tumakai da awakai 300.

Bale Shuwa na cikin KARAMAR Hukumar Jere, jihar Barno.

Kodinetan NEMA na shiyyar Arewa maso Gabas, Bashir Garga ne ya bayyana haka a cikin wan bayani da ya fitar, jiya Lahadi a Maiduguri.

Garga ya kara da cewa: “Maharan da ake zargin Boko Haram ne sun shiga kauyen Bale-Shuwa da ke cikin Karamar Hukumar Jere, da karfe 7:30 na dare, a ranar Asabar.

“An tabbatar da kisan wani gurgu kuma sun kona gidaje 65, sun gudu da shanu 200 da tumakai da awakai 300.”

Ya ci gaba da cewa an yi wa wadanda suka ji raunuka magana, kuma NEMA na ci gaba da tantance wadanda suka yi asara domin sanin irin yadda za a kai musu agajin gaggawa.

Kamfanin Dillancin Labarai NAN, ya ruwaito cewa jama’ar da suka gudu daga kauyen sun koma gida bayan da sojoji suka kori maharan Boko Haram.

Share.

game da Author