Boko Haram sun sace mata 9 a Barno

0

A yau Juma’a ne wani ma’aikacin tsaro na Civilian JTF Ba’a Goni ya sanar wa PREMIUM TIMES cewa Boko Haram sun kai wa garin Bama dake karamar hukumar Bama hari idan a dalilin haka suka kashe wani namiji daya sannan suka sace mata tara.

Ba’a ya bayyana cewa wannan abin tashin hankalin ya faru ne a ranar Laraba bayan wadannan mata sun je gona domin yin girbi.

‘‘Dama a duk lokacin da aka fara girbin amfanin gona mata ne suka fi yin girbi. Sannan a wannan rana kamar yadda aka saba mata shida, ‘yan mata uku da namiji daya sun tafi gona inda Boko Haram suka kashe shi namijin dake tare da su sannan suka tarkata wadannan mata suka tafi da su.

” A yanzu haka hankalin kowa ya tashi a Bama sannan kowa na fargaban fita zuwa gona don girbi domin guje wa fadawa hannu wadannan miyagun mutane.

Ba’a yace Bama gari ne da ta yi shekaru biyu a hannu Boko Haram sannan bayan kwato garin da jami’an tsaro suka yi, Boko Haram kan kai hari garin a duk lokacin da suka samu dama.

Har yanzu dai jami’an tsaro basu ce komai ba game da wannan al’amari.

Share.

game da Author