Majiyar PREMIUM TIMES ta shaida mana a jiya Laraba cewa, Boko Haram sun kai wa sojojin Kasa-da-kasa na Najeriya hare-hare a ranakun 5 da 6 Ga Nuwamba, kuma sun kashe soja daya, 16 kuma sun bace ba a san inda suke ba.
A harin da suka kai wa sojoji a sansanin kauyen Kukawa a ranar 5 Ga Nuwamba, da kuma wata nakiya da ta tashi da wata motar sojoji a Mallam Fatori ranar 6 Ga Nuwamba.
Dukkan wadannan kauyuka su na Arewacin Barno ne kuma su na kan iyaka da Jamhuriyar Nijar.
Boko Haram sun yi kokarin ganin sun yi galaba a wani shingen bincike da sojoji suka kafa a ranar 5 Ga Nuwamba, wanda Sojojin Musamman na 101 da kuma na Bataliya ta 157 ne ke wurin.
Sun kai harin ne wajen 5:40 na yamma.
Sun kori sojojin kuma suka kona motocin daukar sojoji biyu, sannan suka gudu da zabgegiyar bindigar kakkabo jiragen yaki guda daya.
Haka wata majiyar sojoji ta shaida wa PREMIUM TIMES.
Majiyar ta ce daga nan sai Boko Haram suka karasa cikin gine-ginen wata sakandare da aka kaurace ba a karatu a cikin ta, amma sojoji ke amfani da gine-ginen a matsayin sansanin su. Sun kone dakin gudanarwar sansanin kuma suka kone dakin dafuwar abinci da duk abin da ke cikin sa.
A wannan farmakin ne suka kashe soja daya, 16 kuma suka bace, ba a san inda suke ba, har zuwa Laraba da dare babu labarin su.
Sai dai kuma Boko Haram sun tsere yayin da suka ga sojojin sama a cikin helikwafta sun kai dauki.
An rika bin su da helikwafta ana kai musu hari, amma suka tsere suka koma cikin mabuyar su.
Majiya ta ce sojojin sama na can na tantance irin barnar da aka yi, domin mika rahoto a hedikwatar sojoji.