Boko Haram sun kashe kwamandan sojojin Najeriya da wasu sojoji da dama

0

Wasu mayakan Boko Haram, sun yi wa sojojin Najeriya shahadar-kuda, inda suka afka musu bagatatan, har suka kashe kwamandan wani ayarin sojoji da kuma wasu sojojin da aka tabbatar da sun kai dozin da yawa.

Wata majiya ce daga cikin hukumomin tsaro na sojojin kasar nan ta sanar da PREMIUM TIMES labarin wannan mummunan hari.

Majiyar ta kara da cewa maharan sun kuma tsere da dimbin muggan makamai da tulin albarusai a wannan hari da su ka kai wa Bataliya ta 157 da ke Metele, cikin Karamar Hukumar Abadam, jihar Barno.

Sun kai harin ne a ranar Lahadi da wajen karfe 6 na yamma.

Harin dai wani koma baya ne ga kokarin da sojojin Najeriya ke yi wajen ganin an fatattaki Boko Haram daga Arewa maso Gabacin kasar nan.

Akwai fargabar makomar sojojin da ke wannan sansani, wanda ko cikin wata daya da ya wuce sai da Boko Haram suka kai masa hari.

A yanzu kuma hukumar tsaro ta sojoji na ta kokarin shawo kan damuwar da harin ya haifar, ta hanyar shirin sabon harin kakkabe Boko Haram na game-gari, na musamman.

PREMIUM TIMES ta gano cewa har zuwa yau Talata da safe ana ta kokarin tsinto gawarwakin sojojin Najeriya, ana kwashe su daga wurin da aka kai musu harin.

Sai dai kuma wannan majiyar ba ta iya fayyace yawan Boko Haram da aka kashe a wurin gumurzun ba.

Majiya ta ce wanda aka kashe din wani Laftanar Kanar ne, wanda ya dade ya na jagorantar ayarin rundunar.

An ce ya taba kin tattara sojoji su fita yaki da Boko Haram, yayin da shi kuma ya bayyana dalilin sa na rashin makamai marasa garambawul.

PREMIUM TIMES ta ki bayyana sunan Laftanar Kanar din da aka kashe, saboda ba ta san ko hukuma ba ta kai ga sanar da iyalan mamacin ba.

Idan ba a manta ba, Boko Haram sun kai wa wannan sansani mummunan hari, a ranar 8 Ga Oktoba, har suka kashe sojoji 18, suka ji wa wasu 8 raunuka. PREMIUM TIMES ta ruwaito muku wancan hari da aka kai.

An kuma akalla sojoji 157 ne suka bace lokacin, kuma har ya zuwa yau sama da wata daya, hukumomin sojoji ba su yi wani cikakken bayani gamsasshe dangane da makowar wadannan sojoji 157 ba.

A wannan hari sojoji sun amince da cewa an kai musu hari, amma hukumar sojojin ta yi nuni cewa asarar rayukan da aka yi, ba su yi yawa ba.

Yayin da Boko Haram ke ci gaba da kai munanan hare-hare a kan sojoji, ita kuma gwamnatin Buhari sai hakikicewa ta ke yi cewa ta shawo kan yaki da Boko Haram.

Share.

game da Author