Boko Haram sun dandana kudar su a hannun sojojin Najeriya a Arege, jihar Barno

0

Dakarun Najeriya sun fatattaki mayakan Boko Harama da suka nemi yi wa wani sansanin sojojin Najeriya dake kauyen Arege, Jihar Barno shigar bazata.

Kafin Boko Haram su ankare sojojin Najeriya sun bude musu wuta inda suka ragargaza su. Da yawa daga cikin Boko Haram din sun arce wasu kuma da dama sun sheka lahira nan take.

Sojojin Najeriya sun kwato makamai da dama a wannan batakashi da suka yi.

Share.

game da Author