Hafsan Hafsoshin Sojojin Sama, Abubakar Sadique, ya bayyana cewa sojojin sama za su girka sansanin makamai a Difa cikin Jamhuriyar Nijar, domin kai wa Boko Haram hari.
Abubakar ya bayyana haka a lokacin da ya ke jawabin rufe taron masana na duniya a kan harkokin tsaron kasa ta sararin samaniya a Abuja, a ranar Laraba.
Ya ce wannan sansani da za a kafa zai kawo wani sabon salon samun nasarar kakkabe hare-haren Boko Haram a Arewa maso Gabas.
Sannan kuma ya bada albishir cewa akwai karin hadin kai da goyon bayan da ke tafe daga wasu kasashe na Turai, Gabas Ta Tsakiya, Asiya da Amurka da ma Afrika.
Ya ce shiri ne da za a yi wa matsalar Boko Haram taron-dangin magance ta gaba daya, domin yaki da ta’addanci abu ne da ya buwayi duniya.
Ya kuma shaida wa manema labarai cewa babu kasar da za ta iya yaki da ta’addanci ita kadai. Ya ce sai an hada da taimako da goyon bayan jama’ar da ke da irin wannan matsalar kuma suka fahimci irin barazanar da ta’addanci ke da shi nan gaba a gare su.
Ya ce daga yanzu jiragen yaki za su rika tashi daga Difa cikin Jamhuriyar Nijar su kai hare-hare kan Boko Haram su koma. Maimakon a ce sai sun tashi daga Maiduguri sun kai hari, kuma su sake komawa Maiduguri.