BOKO HARAM: An yi tankade da rairayen canja manyan sojoji 102

0

Hukumar Tsaro ta Sojojin Najeriya ta canja manyan sojoji 103, ciki har da Babban Kwamandan Operation Lafiya Dole da wasu Manyan Kwamandojin Yakin Boko Haram.

Sanarwar da Kakakin Yada Labaran Hukumar Tsaro ta Sojoji, Texas Chukwu ya bayar, ya ce an yi canjin ne domin a saka sabbin jini a cikin shirin jagorancin yaki da Boko Haram da kuma kara shigar da kwararru wajen samun kyakkyawan sakamako.

A yanzu sakamakon wannan canje-canje da aka yi, Manjor Janar Benson Akinroluyo ne sabon Kwamandan Babbar Rundunar Operation Lafiya Dole.

Kafin wannan sabon mukamin kuwa, Benson shi ne Kwamandan GOC Runduna ta 3 da ke Jos.

Ya canji Manjo Janar Abba Dikko, wanda yanzu aka maida shi Shugaban Bangaren Kula da Dangantakar Sojoji da Fararen Hula.

An maida Manjo Janar Nuhu Angbazo zuwa Kwamandan GOC na Jos.

Share.

game da Author