Daya daga cikin wadanda ake zargi da salwantar da naira biliyan 11 tare da tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shema, ya bayyana wa kotu cewa jami’an EFCC ne suka tirsasa shi goga wa Shema bakin fenti.
Ana zargin Shema da wasu mutane hudu da salwantar da naira biliyan 11.
Mutumin mai suna Ibrahim Dankaba, ya shaida Mai Shari’a Maikaita Bako ta bakin lauyan sa cewa EFCC ce ta yi masa barazana da tsorata shi cewa lallai sai dai ya jefa sunan Shema a cikin harkallar a lokacin da ya ke rubuta bayanan sa.
Haka lauyan sa Napoleon Idanele ya shaida wa kotu a madadin sa.
Daga nan sai mai shari’a ya dage sauraron karar zuwa ranar Laraba, domin ci gaba da sauraren kara a cikin kara.
Kafin nan dama sai da mai gabatar da kara, O.I.Uket, ya gabatar da shaidu biyu, Abubakar Haruna da kuma Habu Muhammad, dukkan su jami’an EFCC.
Sai dai kuma sun bayyana wa mai shari’a cewa ba a tirsasa wanda ya rubuta bayanan ko yi masa wata barazana ba.
Sun ce don radin kan sa ya rubuta, kuma babu wani yanayi na takura a kan sa a lokacin.