Bayan shekara biyu da shigar da karar likitocin da suka yi sanadiyyar rasuwar wata mara lafiya, kotu bata zauna ba

0

Shekaru biyu kenan da lauyen Portia Sambo, Charles Abalaka ya shigar kan sakacin da likitoci a asibiti a babbar kotun tarayya dake Abuja, kotun bata zauna ba.

Idan ba a manta ba a 2016 ne Portia Sambo ta rasa ‘yar ta mai suna Sandar David a dalilin sakacin da likitocin asibitin gwamnati dake Abuja suka yi.

Wata ‘yar uwar Sandara mai suna Sophia ta bayyana wa wakiliyar PREMIUM TIMES cewa Sandara ta je wannan asibiti ne saboda matsalar da ta samu da maranta.

” Garin yi mata fida ne wadannan likitoci suka huda huhu ta sannan suka ki bayyana mana har Allah ya dauki ranta.

Ta ce a dalilin haka ne suka shigar da kara a kotu inda suke bukatar kungiyar likitoci MDCN ta biya su kudin diyya har Naira miliyan 50.

Tun daga wannan lokaci kotun da aka shigar da wannan kara ta rika daga ranar sauraron shari’ar.

Share.

game da Author