Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa badun Allah ya kawo wannan gwamnati ba da irin ta’adin da Boko Haram za su yi a kasar nan ba shi misaltuwa.
Buhari ya ce zuwan gwamnatin sa ne ya sa aka samu nasara matuka kan ayyukan Boko Haram da hare-haren da suke tayi a sassan kasar nan.
” Dole mu rika tunatar da kan mu yaya muke a da da kuma yanzu game da Boko Haram. Mutanen jihar Barno sun san irin namijin kokarin da muka yi a cikin shekara uku da suka wuce, sune shaida.
” Wannan yaki ne da dole mu yi nasara a kai. Ina kira ga dakarun mu da su toshe kunnuwar su ga dukkan irin maganganun batanci da ake yi, su maida hankali wajen ganin an kau da wadannan miyagun mutane daga doron kasa.
” A matsayi na na shugaban kasa mai cikakken iko, zan yi iya kokarina wajen ganin na samar muku da dukkan abubuwan da kuke bukata domin samun nasara a wannan yaki da suka hada da makamai da sauran su. Sannan kuma dole ne in tabbatar an samu tsaro a ko-ina- a fadin kasar nan a dalilin haka dole kuma sojojin mu ku maida hankali wajen ganin hakan ya tabbata.
” A dalilin haka nake kira ga shugabannin hukumomin tsaron kasar nan da su hada kai wajen ganin an dakile duk wani shiri da zai wargaza zaman lafiya da kuma ayyukan ta’addanci da na rashin tsaro a ko-ina a kasan.
Buhari ya kai ziyara asibitin Maimalari dake Maiduguri domin duba sojojin da suka samu rauni a harin Boko Haram. Bayan nan Kuma ya ziyarci fadar mai martaba Shehun Barno.
Idan ba a manta ba daya daga cikin sojojin da suka tsira daga harin da Boko Haram suka kai wa barikin Metele, karamar hukumar Guzamala jihar Barno ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa shima Allah ne yasa zai tsira da ran sa a wannan hari domin kuwa sojojin Najeriya da ke aiki a wannan bariki basu sha da dadi ba.
Ko da yake tun kafin wannan hari, sai da Boko Haram suka aika wa Sojojin sakon cewa zasu kawo farmaki barikin. Ba nan ba kawai har da wasu dake Kauyukan Barno.
” Boko Haram sun far wa barikin mu ne ranar litini da misalin karfe 6 na yamma.
” A lokacin da sojan da ke can kololin sama wato mai hangen nesa daga barikin ya sanar mana cewa ga fa gungun mayakan Boko Haram nan sun kunno kai zuwa wannan bariki sai dukkan mu muka daura damara muka ja daga muna jiran su.
” Gaba daya batakashin bai dauke mu tsawon mintuna 45 ba domin mayakan Boko Haram din sun fi karfin mu a dalilin manyan makamai da suke dauke da su.
” Da muka fahimci cewa ba za mu yi galaba a wannan batakashi da muke yi da ‘yan Boko Hama din ba sai muka nemi mu gudu. Hakan shima yayi mana wuya matuka domin barikin a zagaye yake da yawa sannan kuma ta hanya daya da ake shiga barikin kuma ta nan ne suke bude mana wuta – Yadda Boko Haram suka yi wa barikin Metele diran mikiya suka kashe sojoji 75.