Shugaban kungiyar ma’aikatan jinyar da suka kware wajen kula da yara kanana ta Najeriya Olubunmi Lawal ta bayyana cewa Najeriya na jerin kasashen duniya uku da suka fi fama da matsalolin haihuwar bakwaini.
Bakwaini sune jariran da ake haihuwa basu wuce wata bakwai a cikin uwayen su ba ko kuma sun wuce amma basu kai watanni tara da ake zaton mace zata haihu ba.
Ta ce bincike ya nuna cewa kasar Sin itace kasar dake kan gaba wajen yawan jariran da ake haifa basukai watannin haihuwa ba sannan sai kasar India da ke bi mata. Najeriya ce ta uku cikin jerin kasashen da ake haihywar irin wadannan jarirai har 773,600 duk shekara.
Ta fadi haka ne a taron ranar Bakwaini da ake yi duk shekara inda ta kara bayyana cewa bincike ya nuna cewa akan haifi bakwaini miliyan 15 a duniya duk shekara inda kashi 60 bisa 100 daga ciki ana samun su ne a kudu da Saharan Afrika.
Dalilai 6 dake sa a haifi da bakwaini:
1 . Shan Taba Sigari
2. Mai dauke da Cutar siga (diabeties) ta Uwa ko ta uba.
3. Amfani da magungunan da wasu mata masu ciki ke yi batare da izinin likita ba.
4. Shan giya.
5. Rashin cin abincin da ya kamata.
6. Yawan rashin samun natsuwa da kwanciyar hankali ga mai ciki.