BACEWAR BILIYOYI: Majalisar Dattawa za ta bincike Hadiza Usman ta Hukumar Kula Da Tashoshin Ruwa

0

Majalisar Dattawa ta bai wa kwamitin kula da Zirga-zirgar Jiragen Ruwa, NPA kwanaki uku kacal domin ta gano inda wasu tulin Naira biliyan 177 da NPA ba ta zuba aljihun gwamnatin tarayya suke.

Wani dan kwamitin ne mai suna Sanata Mohammed Hassan ya ja hankalin majalisar cewa akwai wasu naira biliyan 177 da Hukumar NPA ba ta zuba a asusun gwamnatin tarayya ba.

Daga nan sai ya nemi da a gaggauta binciken shin har yanzu kudaden sun a a hannun NPA, ko kuwa ina suka makale?

Jiya Laraba, Hassan ya ce NPA ta tara kudaden shiga har naira bilyan 303, wadanda ya ce ta kashe naira bilyan 125 a ciki, amma ba ta zuba sauran naira biliyan 177 a cikin asusun gwamnatin taratyya ba.

Hassan y ace dukkan wani kokari da majalisar dattawa ta yi domin hukumar NPA ta bayyana mata inda kudaden suke, ya ci tura.

Ya ce wata bvakwai kenan su na neman a yi musu inda kudaden suka makale, amma an yi watsi da bukatar ta su.

Daga nan sai Shugaban Majalaisar Dattawa. Bukola Saraki ya bada umarnin cewa kwamitin ya gaggauta gano inda kudaden suka shige a cikin kwanaki uku.

Share.

game da Author