Babu bako a cikin masu neman shugabancin Najeriya – Iya ruwa fidda kai a 2019, Daga Mustapha Soron Dinki

0

Alhamdulillah, siyasa ta fara daukar zafi a kasar Najeriya tsakanin many an jam’iyu masu neman mulkin kasar. In Allah yaso siyasar kasarmu ta dauko hanyar gyaruwa duba da yadda adawar siyasa ta samu gindin zama. APC ce jam’iya mai mulki amma tana cikin matsanaicin matsin lamba daga babbar jam’iyar adawa ta PDP.

Atiku Abubakar dai shine ‘dan takarar jam’iyar adawa wanda zai kara da Buhari, wasu daga cikin ‘ya’yan jam’iyar ta PDP suna gani kamar lokacin yin hannun karba hannun mayarwa yazo saidai alamu yana nuna cewa komai yana iya faruwa.

Adawar siyasa tana kawo cigaba, don rashin ‘opposition’ a siyasa baya nuna cigabanta. Mulkin Najeriya akwai dadi shiyasa ba kowa bane yake sauka daga shi ya samu kwanciyar hankali. Nazari yana nuna cewa babu sana’ar da ta kai siyasa riba a kasarmu shiyasa mutane da yawa sun fito neman kujerar mulkin kasar saidai Allah ya taimaki talakawa da makamin kare dangi a filin zabe. Ita ce kuri’a idan sun yi amfani da ita ta hanya mai kyau. Babu wanda bai rike mukami ba an ga kamun ludayinsa tsakanin Buhari da Atiku.

Ban ce maka ka zabi Buhari ko Atiku ba ko kada ka zabesu, amma kamar yadda shi shugaba Buhari ya fada, idan kana da wanda ya fishi ka zabeshi kai tsaye. Atiku yayi mataimakin shugaban kasa a Najeriya har tsawon zango biyu na siyasa. Wannan abu ne mai sauki talaka ya gwada nauyinsu a sikeli tunda kamar yadda na fada an san nauyin kowa a cikinsu.

Wannan dama ce ga masu son cigaban Kansu. An dade ana neman mafita a Najeriya, PDP tayi mulki na shekara 16, ga kuma APC tana yi, talakawa sai su duba, me PDP ta samawa talakawa kafin damar mulki ta kubuce mata? Ko yanzu ne suka hango gyaran suke shirin yi? Sannan ita gwamnatin da take kai me take yi don gina sabuwar Najeriya.

Wannan hisabin yakamata ka yi kafin ka dangwala babban yatsanka akan kuri’ar zabe. Idan kuma siyasar kudi kafi so, to ga fili ga mai doki nan. Kai da wahala kun auri juna.

Najeriya ta dade a cikin siyasar kudi, amma ni dai bansan mutum daya da yaci ribarta ba ban kuma ce babu ba. Mafi munin abun shine, su baku kudin ku kashe daga baya kuma ku dawo talaucinku. Tun 2003 wasu suka mayar da siyasar kudi Sana’a, suke kwaso mata da maza masu mutuwar zuciya ana basu kudi kadan suna zabar mutumin da basu sani ba a mu’amilance.

Kuma da yawancin su sun fi kowa shan wahalar Najeriya saboda sun zama “su basu dauko ba, su ba’a daukosu ba” Allah ya rabamu da abunda ba riba kuma ba lada. Muna bayar da shawara ga talakawa wadanda jikinsu yake gaya musu a siyasar Najeriya da su saka nutsuwa don Najeriya ta gyaru da ikon Allah. Ku zo mu yi iya yin mu, kammala ta Allah ce, idan yaso sai kasar ta gyaru.

Allah yasa mu ga Alheri.

Share.

game da Author