Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta bayyana cewa ilimantar da yara mata makami ne wajen kawar da matsalolin da mata kan yi fama da su a dalilin auren wuri.
Ta ce wadannan matsaloli kuwa sun hada da rashin samun ilimin boko, yoyin fitsari, talauci da sauran su.
Kakakin Aisha, Suleiman Haruna ya sanar da haka yayin da kungiyar matan dake aiki da gwamnatocin na yankin kasashen Afrika suka ziyarce ta a fadar shugaban kasa ranar Laraba a Abuja.
” Ilimantar da yara mata zai taimaka musu wajen samun daman zaban yadda za su tafiyar da rayuwarsu bayan sun yi aure musamman a fannin tsara hanyoyin kubutar da kansu daga talauci.
A Karshe Aisha ta yi kira ga kungiyar da su tsara hanyoyin wayar da kan mata game da mahimmancin samun ilimin Boko tare da yin la’akari da banbancin al’adun bangarorin kasashen Afrika.
Sannan kungiyar ta tsaro hanyoyin kawar da matsalolin yin auren wuri da mata da dama ke fama da su domin inganta su.