Dan takarar jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa na 2019, Atiku Abubakar, ya gana da shugabannin kabilar Igbo, inda ya sha alwashin zai sake farfado da arzikin Najeriya.
Abubakar ya bayyana haka a taron da ya yi da shugabannin kabilar Igbo a Enugu jiya Laraba.
Ya ce ya damu da irin halin da Najeriya ke ciki, da kuma makomar kasar nan da kuma abin da ‘yan bayan mu da ba ma kai ga haifa ba za su iya taraswa nan gaba.
“Ya zama tilas mu hada hannu mu saita tattalin arzikin mu. Don haka ina kira da ku amince min ni da Peter Obi za mu iya saisaita Najeriya.
Atiku ya ce ya damun kwarai da irin yadda Kudu maso Gabas ta zama koma baya wajen ababen more rayuwan jama’a a yankin.
Tun da farko shugaban kungiyar Ohaneze Ndigbo, Nnia Nwodo ya koka da rashin ayyukan ci gaba da babu a yankin Kudu maso Gabas.
Ya ce an ki tafiya tare da yankin a cikin lamurran tafiyar da kasar nan, kuma an yi nade naden mukamai a kasar wadanda ya ce ba a yi wa yankin na su adalci ba.
Shi ma da ya ke jawabi, Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya yi kira gare su da su goyi bayan Atiku, domin ba zai taba yi musu butulci ba.
Discussion about this post