Mai martaba sarkin Awe, Jihar Nasarawa Abubakar Umar II ya rasu.
Darektan Yada Labaran gwamnan jihar Nasarawa, Yakubu Lamai, ne ya sanar da haka da yake zantawa da kamfanin dillancin Labaran Najeriya a Lafiya.
Lamai ya ce marigayi Abubuakar ya rasu ne bayan fama da yayi da ‘yar gajeruwar rashin Lafiya a wani asibiti dake Abuja.
Tuni dai har an yi jana’izan marigayin.
Shima gwamnan jihar Nasarawa, Tanko Almakura ya mika sakon jajen sa ga iyalai da masarautar Awe bisa wannan babban rashi da aka yi.