Hukumar ‘Yan sanda ta kori wani jami’in ta mai suna Kadima Useni, sakamakon kama shi da aka yi ya sha barasa ya yi mankas a wurin aiki.
Useni wanda dan sandan kwantar da tarzoma ne, watau mobal, ya na a cikinn runduna ta Squardron 22 ce da ke Ikeja, Lagos, kuma an kore shi a jiya Laraba.
Kakakin Yada Labarai ta Jihar Lagos, Chike Oti ce ta bayyana haka, bayan da aka kama Useni.
An kama shi ne bayan da aka rika watsa wani bidiyo ta WhatsApp da kuma Facebook, mai nuna dan sandan mankas, ya na tangadi da magaro a cikin unguwar Dopemu da ke Lagos.
Sanarwar ta ce an sanar wa Sufeto Janar na ‘Yan sanda, Ibrahim Idris, cewa an kama Useni a layin Akonwonjo, cikin unguwar Dopemu ya sha ya bugu kuma ya na tambele.
Ta ce nan take Sufeto Janar ya umarci Kwamishinan ‘Yan Sandan Lagos ya kori Useni daga aiki.
Kwamishina Ihodimi Edgal ya ce an kama Useni ya sha barasa mai tarin yawa, kuma ya yi talil a jiya Laraba, 7 Ga Oktoba, 2018.
Useni wanda Insifekto, ya na da lambar daukar aiki ta 176219.
Bayan an kama shi, ya tabbatar da cewa shi ne a cikin bidiyon, inda nan take aka rubuta masa takardar sallama.
Bayan nan kuma, Kwamishinan ‘Yan sanda ya umarci shugaban rundunar da ya gaggauta rufe duk wani gidan giya da ke kusa a ‘yan sandan a wannan unguwar.
Daga nan kuma ya hori jama’a da su daina bai wa jami’an ‘yan sanda kyautar barasa, domin idan sun sha, ba jiri kadai ta ke sa su ba, har hankulan su na gushewa a lokacin.
Discussion about this post