An janye dokar hana walwala a garin Kachia

0

A yau Alhamis ne gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da janye dokar hana walwala a garin Kachia.

Kakakin gwamna Nasir El-Rufai, Samuel Aruwan ya sanar da haka a Kaduna inda ya bayyana cewa gwamnati ta yi haka ne ganin yadda zama lafiya tabbata a garin.

Sai dai Aruwan ya ce dokar hana walwala daga karfe 6 na safe zuwa 5 na yamma na nan haryanzu daram garuruwan Kasuwan Magani da Kujama.

“Bayan tattaunawar da gwamnati ta yi da jami’an tsaro a jihar gwamnati ta amince a ci gaba da bin dokar hana walwala a Kujama da Kasuwar Magani har sai an gamsu cewa zaman lafiya ya dawo matuka.

Share.

game da Author