An gudanar da taro don samar da matsaya game da rashin dakunan bahaya a Najeriya

0

A ranar Alhamis ne Asusun tallafa wa kananan yara na majalisar dinkin duniya (UNICEF) ta kammala taron samun madafa game da illolin dake tattare da yin bahaya a waje musamman a kasuwannin kasashen nahiyar Afrika.

UNICEF ta tattauna da gwamnatocin kasashen nahiyar Afrika da kugiyoyin da hada kawance da su domin tsara hanyoyin kawar da Illolin bahaya a fili.

A Najeriya akwai mutane miliyan 46.5 da ke yin bahaya a waje wanda hakan yasa kasar ke yawan fama da cututtuka kamar su kwalara, Zazzabin tafot da sauran su .

Jami’ar UNICEF Ms Marie-Pierre Poirier ta ce a dalilin haka suka shirya wannan taro domin wayar wa mutane kai game da wannan matsala da samar da yadda ya a kare yara kanana daga fadwa hadarin wannan mummunar abu.

‘‘Burin mu shine daga nan zuwa 2030 mun samar da tsaftataccen muhalli da bandakuna a kasuwanni a kasashen nahiyar Afrika domin kawar da yin bahaya a waje.

A karshe Poirier ta ce za su hada hannu da gwamnatocin nahiyar Afrika, kungiyoyi masu zaman kansu domin samar da ci gaba don ganin sun cin ma burin su.

Share.

game da Author