An gudanar da taro don inganta ayyukan gwamnat a Abuja

0

A yau Alhamis ne cibiyar ‘Development Research and Projects Centre (dRPC)’, kungiyar ‘Women in Media (WIM) da kungiyar Advocacy in Child and Family Health At Scale suka shirya taron hada kawance tsakanin gwamnati da mutane domin samar da ci gaba a aiyukkan gwamnati da gwamnatin jihar Kano ke yi musamman a fannin kiwon lafiya.

Taron ya gudana ne a garin Abuja sannan wakilan gwamnatin jihar Kano da kungiyoyi da dama ne suka harlaci taron.

Bayanai sun nuna cewa gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya sa hannu a takardar wannan shiri domin gwamnatin jihar ta sami shiga wannan shiri a watan Agusta.

A yanzu haka jihohin Kaduna da Anambara sun shiga wannan tsarin.

Jami’ar wannan shirin Halima Ben Umar ta bayyana cewa shirin zai samar wa gwamnati da mutanen da ake shugabanta damar tattauna hanyoyin samar da ci gaba da kuma hanyoyin kawar da matsalolin da ake fama da su a ayyukan gwamnati da fannonin gwamnati musamman fanonin da suka shafi inganta mutane.

A taron Halima ta dauki dogon lokaci domin kara yawar mutane kai game da wannan shiri da mahimmancin da yake tattare da shi.

Za a kammal taron ranar Juma’a a otel din Corinthia Hotels dake Garki Abuja.

Share.

game da Author