Akwai yiwuwar tabbatar da gano kaburburan sojojin Najeriya 650 da aka kashe a lokacin Yakin Duniya na Biyu, a kasar Burma, wadda a yanzu ake kira Myanmar.
Idan har hakan ta tabbata kuwa, to yawan adadin sojojin da a baya gwamnatin Najeriya ta ce sun mutu a Burma ya nunka sau goma kenan.
Kafin makon da ya gabata, gwamnatin Najeriya ta bada rahoton tabbatar da cewa sojoji 63 ne kadai aka kashe wadanda suka yi yaki a karkashin Burged ta Afrika ta 82 a karkashin Sojojin Mulkin Mallaka na Birtaniya.
Cikin makon da ya gabata dai Sabon Jakadan Najeriya a kasar Thailand da Myanmar, Ahmed Bamalli, ya ziyarci Shugaban Kasar Myanmar, Win Myint, domin kai masa wasikar shaidar turo shi aiki a kasar da Gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi.
Sai dai kuma yayin da sabon Jakadan Najeriya a Thailand da Myanmar, Ahmed ya kai ziyara, an dauke shi an zagaya da shi cikin mashahuriyar Makabartar Sojojin Yakin Duniya na Biyu da ke Yangon a birnin Rangoon.
Daya daga cikin hadiman jakadan Najeriya, ya dauki hotunan kaburburan da ke cikin makabartar, kuma ya tura wa PREMIUM TIMES.
A cikin makabartar akwai kaburbura za su kai 6,000. Kuma wani mai zagayawa da jakadan ya nay i masa bayanai, ya shaida wa Bamalli cewa akalla akwai kaburburan sojojin Najeriya a wurin za su kai 650 a cikin wata makabartar a cikin kasar.
Shi ma Bamalli ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa a makabartar Rangoon ya ga kaburburan sojojin Najeriya da dama, kuma jami’an kula da makabartar sun shaida masa cema akwai kaburburan wasu ‘yan Najeriya da yawan gaske a cikin wata makabartar.
Ya ce zai sake komawa Myanmar domin ya yi kokarinn gano wannan makabarta da aka magana, domin ta hakan ne zai iya bayar da sahihin adadin sojojin da aka binne a makabartun.
Amma dai ya ce da idon sa sun ga kaburbura 25 na sojojin Najeriya a makabartar Rangoon.
Yawancin wadannan sojoji, duk daga Arewacin Najeriya aka dauke su aka kai su Yakin Duniya tare da sojojin Arewacin Ghana, inda sojojin Birtaniya suka yi yakin korar Japanawa daga mamayar da suka yi wa Burma, wato Myanmar ta yanzu tsakanin 1942 zuwa 1945.
Yawancin wadanda aka yi wa kwasar-karan-mahaukaciya aka zuba aikin soja a lokacin, yara ne kanana, wasu ma bas u wuce shekaru 16 ba. Sun rika yin aikace-aikacen wanke-wanke, daukar kaya zuwa dafa abinci da sauran ayyukan da suka jibinci gyare-gyaren motoci.
Discussion about this post