An daku a wajen rabon kyautar naira 300,000 da Badaru ya ba ‘yan kungiya

0

Wasu ‘yan kungiya da suka kai 40 sun daku da juna a wajen rabon kudi da gwamnan jihar Jigawa ya basu su raba bayan sun kai masa ziyarar nuna goyon baya.

Su dai wadannan yan kungiyar sun kai wa gwamna Badaru ziyarar nuna goyon baya ne.

Bayan sun gana da gwamnan sai ya basu naira 300,000 su sha ruwa.

Daga nan ne fa komai ya yamutse, inda kowa ya nemi a bashi rabon sa. Kafin ka ace wata-wata an kicime da dambe. Kai rikici dai ya kaure abu kamar a fim din Indiya har sai gashi wani da aka doddoke wa baki cikin shugabannin sai da jami’an yan sanda suka zakuloshi cikin rubibi yana shan ribiti.

Da yawa dai sun koka da yadda shugabannin kungiyoyin suka nemi danne kudinne inda wasu suka ga ba zai sabu ba.

Share.

game da Author