A yau Talata ne gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da dage dokar hana walwalan a cikin garin Kaduna ranar 31 ga watan Oktoba.
Kakakin gwama Nasir El-Rufai Samuel Aruwan ya sanar da haka a Kaduna inda ya bayyana cewa gwamnati ta yi haka ne ganin yadda zama lafiya tabbata a jihar.
Aruwan yace dokar hana walwalar zai ci gaba da aiki a garuruwar Kujama, Kasuwan Magani da Kachia.
” Dokar hana walwalan zai ci gaba da aiki daga karfe 10 na dare zuwa karfe 6 na safe a Kachia sannan da karfe 5 na yamma zuwa 6 na asuba dokar za ta cigaba da aiki a Kasuwan Magani da Kujama’’.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da sassauta dokar hana walwala a fadin jihar.
Kakakin gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai, Samuel Aruwan ne ya sanar da haka a Kaduna.
Aruwan ya bayyana cewa babban dalilin da ya sa gwamnati ta sassauta tsawon lokacin dokar shine ganin yadda zaman lafiya ya dawo matuka a tsakanin mutanen jihar.
” Daga yau Laraba dokar ta bada dama mutane su gudanar da harkokin su tun daga karfe 5 na safe zuwa karfe 10 na dare.”
Yanzu kowa zai ci gaba da harkokin sa ne tun daga safe har zuwa karfe 10 na dare a kullum.
Idan ba a manta ba a wannan makon ne gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da sassauta dokar hana zirga-zirga a fadin jihar.
A sanarwan da Kakakin gwamnan jihar Samuel Aruwan ya fitar ranar Lahadi cewa daga ranar Litini 29 ga watan Oktoba, za a rika walwala daga karfa 6 na safe ne zuwa karfe 5 na yamma.
Sannan kuma gwamnati ta yi kira ga hukumomin jiragen Sama da na Kasa da su dawo da ayyukan su na jigilar fasinjoji zuwa garin Kaduna.
Takardar ta ce bankuna da ma’aikatu za su bude daga wannan rana kuma.
Discussion about this post