Jaridar ‘The Telegraph’ ta nada Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje Gwarzon Gwamnoni na Shekarar 2018 duk kuma da zargin wawurar milyoyin daloli da aka nuno shi a cikin wani bidiyo ya na yi.
Jaridar ta ce ya samu lambar yabon ne a kokarin da ya yi a fanonin inganta shirin kiwon lafiya da kuma harkokin ilmi a jihar Kano.
Ganduje ya shiga tsomomuwa tun bayan da wata jarida mai suna ‘Daily Nigerian’ ta fallasa wasu bidiyo inda ya nuna shi ya na karbar damman daloli yana karkacewa ya zira su a aljihun jamfar sa.
Majalisar Dokokin Jihar ta kafa kwamitin bincike, inda har ta gayyaci babban editan jaridar, Ja’afar Ja’afar ya bayyana a gabanta.
Mako daya bayan an gayyaci Ja’afar, kwamitin ya kuma gayyaci gwamna Ganduje, amma ya noke, bai je ba, sai ya tura wakili.
Ana cikin haka kuma sai wani lauya mai suna Muhammad Zubair, daga kungiyar lauyoyi ta SDN, ya shigar da kara, ya nemi a dakatar da binciken da majalisar Kano ke wa Ganduje.
Kwamiti a karkashin shugabancin Baffa Dan’agundi ya ce zai ci gaba da bincike duk da karar da aka shigar.
Daga baya kuma mai shari’a A.T Badamasi na Babbar Kotun Kano ya sake bada umarnin a dakatar da bincike.
Bayan dakatar da binciken ke da wuya kuma, sai Ganduje ya maka Ja’afar Ja’afar da jaridar Daily Nigerian kara kotu, ya na neman a biya shi diyyar bata masa suna har ta naira bilyan uku.
Shi ma Shugaban Hukumar EFCC ya kira wani taron ‘yan jarida, ciki har da Jaafar Jaafar. A lokacin taron, an yi masa tambaya a kan me EFCC ke ciki game da zargin da aka yi wa Ganduje domin an nuno shi ya na karbar kudade?
Maimakon Magu ya amsa tambayar, sai ya ce a wuce wannan tambayar, a yi masa wata tambaya.
Ba za a iya gurfanar da Ganduje a kotu ba saboda ya na kan mulki, amma za a iya bincikar sa.
Kamar yadda aka binciki tsohon gwamna Ayo Fayose lokacin ya na kan mulki, sai da ya sauka sannan EFCC ta kama shi.
A wurin karrama Ganduje, Manajar Darakta na The Telegraph, Funke Egbemode, ta jinjina wa Ganduje sosai.
Funke har ila yau ita ce Shugabar Kungiyar Editocin Jaridu ta Najeriya, NGE.
Funke ta ce a cikin ‘kiftawar idanu’ Ganduje ya inganta harkokin ilmi da kiwon lafiya a jihar Kano.