Gwamnatin Amurka ta nuna matukar damuwar ta dangane da hargitsin da ya barke tsakanin mabiya Shi’a masu zanga-zanga da kuma sojojin Najeriya a cikin Abuja da kewaye.
An kashe masu zanga-zanga da dama, a tsakanin Asabar zuwa ranar Talata, bayan da sojojin suka zargi an rika jifar su da dutse da sauran wasu makaman hannu da harbi da gwafa.
Cikin wani jawabi da Ofishin Jakadanci Amurka a Najeriya ya buga a shafin sa na internet, Amurka na yin kiran da a gudanar da bincke mai tsanani da musabbabin barkewar hargitsin.
“Mu na kira da hukumomin Gwamnatin Najeriya da a gaggauta gudanar da bincike tare da daukar tsatstsauran mataki kan wadanda ke da laifi karya dokar Najeriya. Sannan kuma mu na kiran bangarorin biyu kowa ta daina.”
Kimanin mabiya Shi’a 491 aka kama, kuma a ranar Alhamis aka gurfanar da 120 daga cikin su a kotu, a Abuja.
Discussion about this post