Kungiyar Jinkai ta Duniya, Amnesty International, ta yi tir da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari dangane da yadda sojoji ke ta kashe mabiya Shi’a da ke zanga-zanga a Najeriya.
Masu zanga-zangar dai na neman a saki jagoran su da gwamnati ke tsare da shi tun cikin Disamba, 2015.
“A bisa dukkan alamu dai sojojin Najeriya sun fi karkata wajen shigo da dabarar yi wa masu zanga-zanga kisan gilla idan aka shiga batun mabiya Shi’a.”
Kungiyar ta nuna damuwar ta akan yadda aka kashe masu zanga-zanga kimanin 45 a cikin kwanaki biyu a Abuja.
Har ila yau, kungiyar ta kai ziyara a wurare biyar a Abuja da kuma cikinn jihar Nasarawa, inda ake kula da wadanda aka jira raunuka, kuma ta ziyarci makabartu biyu da aka rufe wadanda aka harbe suka mutu.
Ta ci gaba da cewa ta yi hira da wadanda aka ji wa ciwo ta hanyar harbin da sojoji suka yi musu, sannan kuma ta dauki hotuna har da bidoyo na dukkan abin da ya faru.
Darktan Hukumar Amnesty International a Najeriya, Osai Ojigho, ya bayyana irin abin takaicin da suka gani wanda sojoji suka yi wa mabiya Shi’a a cikin kwanaki biyu, wanda ya ce ya saba wa dokar kasa-da-kasa ta kare rayukan dan Adam.
“An harbi wasu a a kai, wasu a wuya, wasu a kirji, wasu a bayan su, wasu a kafada, wasu a kafafu wasu kuma a hannyen su. Irin wannan harbin da aka yi musu ya nuna kenan sojoji da ‘yan sanda ba sun je ba ne domin tabbatar da zaman lafiya a wurin, sun je ne dama domin su yi kisa kawai.”
Yayin da ya ke kara nuna damuwar sa dangane da wayan wadanda suka ji rauni, ya kuma nuna bacin rai kan irin manyan bindigogin da sojoji suka yi amfani da su wajen kisan ‘yan Shi’a, ciki har da mashinga. Ya yi kira da tilas ne gwamnati ta binciki wannan kira da aka yi wa mabiya Shi’a, wanda ya ce dokar laifuka ta kasa da kasa ta kan kan kowa duniya, har kuwa da sojoji.