Akwai yiwuwar rugujewar hukumar NHIS nan da shekara uku – Kwamiti

0

Kwamitin gudanarwar hukumar Inshorar lafiya ta Kasa ta yi kira da kakkausar murya ga gwamnatin tarayya da ta dauki mataki na gaggawa domin kare hukumar NHIS daga rugujewa.

Kwamitin ta bayyana cewa bisa ga bayanan da ta samu game da hukumar, akwai yiwuwar zata iya rugujewa kwata-kwata nan shekaru 3 masu zuwa a dalilin irin harkallar da a ke tafkawa a wannan ma’aikata.

Bayanan binciken da kwamitin ta gudanar sun nuna cewa tun da aka kafa hukumar shekaru 13 da suka wuce cin hanci da rashawa da rashin gudanar da aiyukka yadda ya kamata sun yi wa hukumar katutu da hakan ya sa hukumar ta kasa tabuka wani abin a zo a gani.

Idan ba a manta ba gwamnatin tarayya ta kafa wannan hukuma ne domin sauwaka wa talakawa farashin kudaden asibitin da suke biya.

Sai dai tun da aka yi haka wannan hukumar bata tabuka komai ba.

A yanzu haka kashi 90 bisa 100 a ‘Yan Najeriya basu cikin shirin inshorar kiwon lafiya sannan dan wadanda ke cikin shirin basu samun biyan bukata.

” Tun ba yau ba gwamnati ta dade ta na yi wa mutane romon kunnen cewa za ta fadada aiyukkan da hukumar ke yi domin kulawa da bukatun mutane amma har yanzu shuru ka ke ji.

A dalilin haka kwamitin ke kira ga gwamnati da ta gaggauta daukan mataki idan ko ba haka ba za a wayi gari ne babu wannan hukuma kwata-kwata.

Share.

game da Author