Abubuwan da za a iya wa mamaci don ladar ya isar masa, Tare da Imam Bello Mai-Iyali

0

Abubuwan da za a iya wa mamaci don ladar ya isar masa

AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW

Dukkan ibada ta dukiya ladanta na isa ga mai-rai ko mamaci idan aka aikamasa da shi. Hakanan wasu ibadun gabobi ladansu na isa ga mamaci.

Nassi ya tabbata cewa musulmi na iya sadaukar da ladar wata ibada ga dan-uwansa musulmi a rayuwarsa ko bayan mutuwarsa. Mai rai da mamaci na amfanuwa daga aikin waninsa.

Ladan sadaukarwa ga bawa yana isa gareshi kuma yayi masa amfani. Musulmin da zai sadaukar da wani aiki ga dan-uwansa yana bukatar niyyar sadaukarwa yayin aikin ko kafin aikin.

Hadisa ya ingata akan yima mamaci azumi da niyyar sadaukar da ladan azumin ga mamacin. Yayin sadaukar da ladan ibada, ana so mutum yace:

Allahumma athibni bi rahmatika, waj’al thawabahu li …….. (ma’ana Ya Allah kabani lada cikin rahamarka, kuma ka sanya ladan wannan aiki ga wane).

Amma wasu daga cikin magabata na ganin cewa sadaukar da ladan ibada baya karbuwa daga bare ko dan uwa na nesa, sai dai dan-uwa na kusa kamar da ga mahaifinsa. Wasu malamai naganin rashin dacewar sadaukarwa kamar yadda muka dauketa ayau. Hujjarsu ita ce magabata basu rayu akan
wannan tafarki na sadaukar da ladan sallar su ba, ko azuminsu, ko karatun Alkur’aninsu ga mamatansu ba, kamar yadda mukeyi ayau.

Allah shi ne mafi sani

Share.

game da Author