Abin da ya sa mu ke so Ingila ta maido mana Dieziani Najeriya – Magu

0

Shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Magu, ya bayyana cewa su na nan kan bakan su na ganin Ingila ta maido tsohuwar ministar man fetur, Dieziani Alison-Madueke zuwa Najeriya domin ta amsa tuhumar zargin da ake mata.

Jiya Litinin ne Magu ya bayyana haka a wani taron manema labarai inda yace Najeriya ta gaji da jiran-gawon-shanun jiran kasar Ingila ta hukunta ta.

Alison-Madueke na zaman gudun jijira tun bayan faduwar jam’iyyar PDP zaben 2015.

Kakakin EFCC na riko, Tony Orilade, ya shaida wa NAN a ranar Lahadi cewa an fara shirye-shiryen dawo da Dieziani gida Najeriya, domin ta fuskanci tuhuma.

Ya ci gaba da cewa nan da makonni kadan za a ji inda aka tsaya dangane da nisan zangon da aka ci wajen kokarin ganin an dawo da tsihuwar ministar gida domin a gurfanar da ita kotu.

Magu ya ce, “Mun lura da cewa a can kasar ba tuhumar ta ake yi ba, kuma mu a nan mun gaji da jiran-gawon-shanu. Tunda su ba za su iya gurfanar da ita ba, to mu a nan za mu iya.”

Share.

game da Author