Daraktan Hukumar Kula da Hannayen Jarin Bankuna (NDIC), Umaru Ibrahim, ya ce rashin yi wa dokar NDIC ta 2006 kwaskwarima ce ta sa har yanzu ba a fara biyan masu ajiya bankunan da suka durkushe a cikin kasar nan ba.
Umaru ya ce wadanda suka yi ajiya a bankunan Savannah, Fortis Micro-Finance Bank da Aso Savings and Union Homes su na shan wahala ne saboda sun kasa dawo da makudan kudaden da suka zuba a wadannan bankuna da cibiyar hada-hada da suka durkushe.
Ya ce a haka wadanda suka yi ajiya a durkusassun bankuna za su ci gaba da wahala har sai an yi wa dokar NDIC ta 2006 gyara tukunna.
Daga nan sai shugaban hukumar ta NDIC, ya yi kira ga Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa Mai Kula da Bankuna, Inshora da sauran Cibiyoyin Hada-hadar Kudade, Sanata Rabi’u Ibrahim da ya yi dukkan kokarin da zai iya yi domin a tabbatar an yi wa dokar gyara ta yadda za a biya jama’a kudaden su da suka salwanta a bankunan.