Abba Ali ya zargi gwamnatin Barno da cire fostocin ‘yan PDP saboda zuwar Buhari

0

Dan takaran kujeran Sanata na shiyar Barno ta tsakiya Muhammed Abba-Ali ya zargi gwamnan jihar Barno Kashim Shettima da Atone-Janar na jihar Kaka-Shehu Lawan da cire fostar duk wani dan takara na jam’iyyar PDP a fadin jihar.

Abba-Ali ya fadi haka ne da yake ganawa da manema labarai a Abuja.

” Sanin kowa ne cewa Shettima ya rasa magoya baya sosai a jihar sannan don tsabar kiyayya kwamishinan shari’a na jihar Kakashehu Lawan ya ya rike bi kwararo-kwararo yana sawa a yayyage fostan PDP da duk wani jam’iyya da ba APC ba.

Abba-Ali ya kuma zargi Shettima da shirin yin amfani da jami’an tsaro domin yin magudi a zaben 2019.

Sai dai kuma kwamishina Lawan ya gargadi Abba-Aji da ya iya wa bakin sa, domin idan ba haka ba gwamnati za ta maka shi a kotu idan ya ci gaba da yi mata kazafi.

” Idan ba karya ba, bana ma garin Maiduguri a wannan rana da ayake cewa wai na jagoranci jami’an BOYE su cire fostan yan takara da ba na jam’iyyar APC ba.

Ya ce doka ne a jihar Barno cewa idan jam’iyya ko kuma dan takara ya saka fasta batare da ya biya haraji ba za a cire shi.

A karshe PREMIUM TIMES ta zazzagaya cikin garin Maiduguri kamar su Lagos street, UMTH junction, Polo junction da Eagle Roundabout inda ta ga cewa duk fastar Abba-Ali da dan takaran gwamnan jihar a karkashin inuwar jam’iyyar PDP Muhammad Imam na nan ba a cire su ba.

Share.

game da Author