Wani likitan zuciya a jami’ar koyan aikin likita dake Boston kasar Amurika Ramachandran Vasan ya yi kira ga matasa kan kula da kiwon lafiyar su domin gujewa kamuwa da cutar hawan jini kafin su manyanta.
Vasan ya bayyana cewa kamuwa da cutar hawan jini tun mutum yana matashi na kawo matsalolin shanyewar bangaren jiki da cututtukan dake kama zuciya kafin a tsufa.
Ya ce ya gano haka ne a binciken da ya gudanar kan illolin dake tattare da kamuwa da cutar hawan jini kafin a tsufa.
” Cin abincin dake kawo kiba a jiki, shan taba, giya, yawan cin abincin dake dauke da sinadarin Carbonhydrates, rashin motsa jiki na cikin abubuwan da matasa ya kamata su nisanta kan su da su.
Vasan y ace yin haka zai taimaka wajen inganta kiwon lafiyar mutum gaba daya.