2019: Tunda Asuban farko Buhari zai gama da Atiku – Ali Ndume

0

Sanata Ali Ndume ya bayyana wa Kamfanin Dillanci Labaran Najeriya a Abuja cewa zaben shugaban kasa da za a yi a watan Faburairu mai zuwa kamar anyi an gama nr tunda Atiku ne zai kara da Buhari.

“Kafin zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP ba mu samu cikakken natsuwa ba saboda mun zura ne ido muga waye PDP za ta tsayar.

” Muna ganin cewa Atiku ne ya lashe zaben fidda gwanin hankalin mu ya kwanta kowa ya kama gaban sa domin kuwa aikin gama ya gama tunda dai Atiku ne suka zaba.

” Abinda ya sa muke dan yin dar-dar a lokacin kuwa shine ganin a cikin jerin ‘yan takarar akwai wadanda da su ne suka lashe zaben fidda gwani na PDP da sun taro mana doguwar wasa. Domin kuwa kila da kila ya kai ga bugun daga kai sa gola.

” kawai sai gashi su da kansu sun sa komai ya zo mana da sauki.

” Kowa ya san irin mulkin kama karyar da Atiku ya rika yi a kasar na lokacin yana mataimakin shugaban kasa. Ba a taba yin mataimakin shugaban kasa mai cikakken iko ba a kasarnan kamar Atiku amma ka zo yankin Arewa Maso Gabas, yankin da ya fito, babu abu daya da ya yi wa wannan yanki a tsawon shekara 8 da yayi yana mataimakin shugaban kasa.

” A yanzu haka daidai da buhun shinkafa koda guda ne Atiku bai taba kaiwa a matsayin taimako na gudunmuwa ga mutanen jihar Barno ba.

Ndume ya kara da yin kira ga ‘Yan Najeriya da su nemi littafin da Obasanjo ya wallafa game da mulkin sa a ga da wasu irin kalamai ya kira Atiku da su.

” A yankin Arewa Maso Yamma ne zai ci zabe ko Yankin Arewa Maso Gabas da Allah ya sa a dalilin zuwan Buhari muka iya komawa garuruwan mu saboda Boko Haram.

” Babu fada ba zagi ballantana ya kai ga ko a dambace. APC za ta gudanar kamfen dinta cikin kwanciyar hankali. Mu ba za mu yi rigima da kowa ba. Amma Atiku ba boyayye bane, ‘yan Najeriya na sane da duk abinda yayi a kasarnan kuma zai gani a kwanon tuwon sa kai har ma da miyan sa.

Share.

game da Author