2019: Mata 62 ne suke takarar kujeru dabam dabam a jihar Kano – Hukumar Zabe

0

Hukumar zabe ta kasa INEC ta sanar cewa akalla mata 62 ne za su yi takarar kujeru dabam dabam a zaben 2019 a jihar Kano.

Jami’in hukumar Riskuwa Shehu ya sanar da haka ranar Alhamis da yake ganawa da manema labarai a garin Kano.

Shehu ya bayyana cewa an mika sunayen wadannan matane bayan kammala zaben fidda gwani na jam’iyyu da aka yi.

” Daga cikin ‘yan takara 74 biyu daga ciki mata ne.

Sannan cikin ‘yan takarar gwamna 54 bakwai daga ciki mata ne.

Shehu ya kuma kara da cewa daga cikin sunayen wadanke takaran kujerun majalisar dokoki na jiha guda 718, 37 daga ciki mata ne.

Share.

game da Author