2019: Kada ku sake zaben gwamnatocin da suka fadi ba nauyi, gargadin Abdussalami ga matasa

0

Tsohon Shugaban Kasa na mulkin soja, Abdussalami Abubakar, ya hori matasa da su daina zama su na babatun korafin gwamnati ta gaza.

Maimakon haka, tsohon janar din cewa ya yi kowanen matasan ya tashi ya je ya jefa kuri’a idan zabe ya zo, domin ya kori duk wata gwamnatin da ba ta tsinana masa komai ba.

Daga nan kuma ya koma kan iyayen yara matasa, inda yay i kira gare su da su jajirce wajen ganin sun tabbatar da ‘yan siyasa bas u yi amfani da ‘ya’yan su wajen tayar da fitina a lokacin gudanar da zabukan 2019 ba.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Abubakar ya yi wannan jawabi ne a Jos, yayin da ya ke jawabi wurin wani taro a Cibiyar Sanin Makama da Dabarun Mulki da ke Kuru, a Jos.

Daga nan ya dangata wasu matsaloli da ya ce kan dabaibaye zabe da suka hada da rashin adalci, yin amfani da dandazon jami’an tsaro, tulin jam’iyyu barkatai da kuma jinkirin da ake samu kafin kotu ta yanke hukuncin bai wa mai gaskiya gaskiyar sa.

Ya gargadi jami’an tsaro su daina kuma kada su rika goyon bayan wani bangare a lokacin zabe.

“Bai kamata a ga jami’an tsaro na nuna goyon bayan wata jam’iyya, kamar yadda suka yi a zaben gwamnan jihar Ekiti ba. Yanzu dai maganar ta na kotu. Amma abin da jami’an tsaro suka yi a Ekiti, zai sa da yawan jama’a jin tsoron fitowa su yi zabe a 2019.”

Ya kuma kara da cewa Boko Haram su ma barazana ce ga zabe a kasar nan.

Share.

game da Author