2019: INEC ta gargadi jam’iyyu kada su karya dokokin yakin neman zabe

0

Yayin da zaben 2019 ke ta kara gabatowa, kuma aka saki dabaibayin fara yakin neman zaben shugaban kasa da na Majalisar Tarayya, yakan ya sa INEC yin gargadin cewa kada wata jam’iyyar siyasa ta kuskura ta karya dokokin da INEC ta gindaya a karkashin kundin tsarin mulkin Najeriya kan zabuka da kamfen.

Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu ne da kan sa ya yi wannan gargadin a lokacin da ya ke ganawa da Kwamishinonin Zabe na fadin kasar nan jiya Laraba a Abuja.

Ganin an fara kamfen tun a ranar 18 Ga Nuwamba, INEC ta ce ta gamsu da yadda yanayin kamfen din ke tafiya a kan al’amurran da suka shafi kasa, ba a kan jifa, yarfe, sharri ko tone-tonen silili a kan ‘yan takara ba.

Hukumar ta kuma yi alkawarin rika bin diddigin yadda kowace jam’iyya ke gudanar da yakin neman zaben ta, domin tabbatar da cewa su na tafiya a bisa turbar da aka gindaya, ba su saki hanya ba.

Dokar kamfen dai da ke cikin Dokokin Zabe a Sashe na 95 ta jaddada cea ba a yarda a yi kalaman zagi da batunci ba a taken jamiyya, musamman kalaman cin fuska, wanda zai taba kima ko martabar wani ko tsokanar addini, al’ada, jinsi ko kabilar wani dan takara.

Dokar kuma ta yi hani da rika rubutawa ko furta kalamai na batunci, zagi a cikin shagube ko zagi a cikin habaice-habaice, wadanda za su iya haddasa barkewar rikici.

Yakubu ya ce taron ya tattauna abubuwa da dama da suka jibinci gudanar da ayyukan zaben 2019.

Share.

game da Author