2019: INEC ta cire sama da sunaye 300,000 daga rajistar zabe

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana cire sama da sunaye 300,000 daga rajistar masu jefa kuri’a.

Hakan ya zo ne a wani bangare na shirye-shiryen da hukumar ke ci gaba da yi, domin tunkara da kuma tabbatar da an samu gudanar da sahihin zabe mai inganci a 2019.

Shugaban INEC Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke karbar bakuncin tawagar ECOWAS wadda ta zo domin duba irin shirin da INEC ta yi domin zaben 2019.

Tawagar na karkashin jagorancin Shugaban Hukumar Zabe ta Saliyo, Mohamed Conteh.

Yakubu ya ce an cire sunayen ne bayan da aka yi amfani da na’urar tantance yatsu, AFIS a kan sunayen da aka yi wa rajista da na’ura.

Yayin da ya ce INEC ta fara aikin kakkabe sunayen masu rajistar da ba a bi ka’ida ba, ya kara da cewa tsakanin 6 zuwa 12 Ga Nuwamba za a lika sunayen wadanda suka yi rajista a kasa baki daya, domin kowa ya ga sunan sa, wanda ke da wani korafi kuma sai ya gabatar tun da wuri.

Ya ce za a lika sunayen ne a mazabu 120,000 na fadin kasar nan.

Shugaban na INEC ya roki ‘yan Najeriya su taimaka wa hukumar wajen zakulo sunayen da ba su cancanta a yi musu rajista ba, domin kakkabe su.

Ya kara da cewa tantance hakikakin sunayen wadanda suka yi rajista, ba aikin INEC ba ne ita kadai, sai an hada da goyon bayan jama’a.

“Zan iya tabbatar muku da cewa zaben 2019 shi ne zaben da aka fi yi wa kyakkyawan shiri da tsari a tarihin zabukan Najeriya.” Inji Yakubu.

Share.

game da Author