2019: Hukumar Zabe na da sauran shiri a gaban ta – Jam’iyyar SDP

0

Jam’iyyar SDP ta bayyana rashin gamsuwar ta ga shirin zabe da hukumar Zabe mai zaman kanta ta yi zuwa yanzu game da zabukan 2019.

Jam’iyyar ta shaida wa wasu daga cikin Editocin PREMIUM TIMES a ziyara da ta kawo ofishin ranar Laraba.

Sakataren jam’iyyar na kasa Shehu Gabam ne ya jagoranci wasu daga cikin jiga-jigan jam’iyyar.

A bayanan sa Shehu yace ” idan dai maganar gaskiya za ayi alamu sun nuna cewa akwai sauran aiki a gaban hukumar zabe ta Kasa game da zaben 2019 da ya tunkaro kai. Ga dukkan alamu hukumar Zabe mai zaman kanta bata shirya wa zabe mai zuwa ba.

Gabam ya ce maganan tsaro da yadda hukumar ke hada kai da jami’an tsaro a lokacin zabe da yadda a ke jigilar kayayyakin zabe sannan da kamayamayar da ya kanannade maganan kasafin kudin da za ayi amfani da su a lokacin zabe da har yanzu ba a kammala tantance shi ba duk suna daga cikin abubuwan dake ba jam’iyyar tsoro a shirin hukumar.

” Idan aka duba yadda hukumar ta gudanar da zabukan jihohin Osun da Ekiti da kuma wadanda aka yi a jihohin Bauchi da Katsina za ka tabbatar cewa lallai hukumar ba ta shirya wa zaben 2019 ba.

” Idan aka duba yadda aka yi wasa da kudi a wadannan zabuka da kuma yadda jami’an tsaro suka yi ta muzguna wa masu zabe zaka tabbatar cewa akwai sauran rina a Kaba. Sannan kuma ko a wajen maganar wayar wa mutane kai za ka ga shi kan sa ma ba a yi. Ba zan iya tuna lokacin da hukumar wayar da kai ta kasa ta gudanar da wani shiri don wayar wa mutane kai game da zabe ba.

Bayan haka Gabam ya kara da cewa wadannan matsaloli da ya ambato da wadanda ma bai ambato ba duk suna daga cikin ababen da ya sa yake ganin hakika hukumar zabe bata shirya wa zaben 2019.

A karshe Gabam ya yi kira ga hukumar da ta maida hankali matuka wajen like duk kafofin dake yoyo da wadanda ake ganin sun cancanci gyara a gyara su kafin zaben.

Shehu Gabam and PT

Shehu Gabam and PT

Share.

game da Author