2019: El-Rufai ya zabi Hadiza Balarabe mataimakiyar sa

0

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya zabi Hadiza Balarabe a matsayin maraimakiyar sa.

Idan ba a manta ba, mataimakin gwamnan jihar Barnabas Bantex ya ce ba zai ci gaba da zama mataimakin gwamnan jihar ba idan wa’adin mulkin su ya kara a 2019 cewa zai koma yayi takarar Sanata ne na yankin Kaduna ta Kudu.

Dr Hadiza Balarabe yar asalin yankin Kaduna ta Kudu na daga karamar hukumar Sanga.

Yanzu haka itace shugaban Hukumar Kula da Kiwon Lafiya a matakin Farko na jihar Kaduna.

A takardar sanar da haka da Samuel Aruwan ya saka wa hannu, El-Rufai ya ce yayi haka ne kara jawo gwamnati da gwamnatin sa ke kokarin yi.

Hadiza ta yi aiki a jami’ar Ahmadu Bello da kuma fannin kiwon lafiya a Babban Birnin Tarayya.

Share.

game da Author