2019: Buhari ya yi alkawarin gyara makarantu 10,000 a duk shekara idan aka sake zaben sa

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alkawarin cewa idan har aka sake zaben sa karo na biyu a zaben 2019, to zai rika gyara makarantu 10,000 a kowace shekara.

Buhari ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya ke kaddamar da kamfen din sa na fara yakin neman zaben 2019, inda ya kaddamar da wani daftari mai suna “Next Level”.

An gudanar da taron ne a Babban Dakin Taro na Fadar Shugaban Kasa, a Abuja.
Ya jaddada cewa idan aka sake zaben sa, to zai maida hankali wajen kara inganta harkokin ilmi sosai.

Ya kuma ce za a kara wa malamai kwarin guiwa ta hanyar inganta sanin makamar aikin su wajen shigo da hanyoyin zamani domin koyo da kuma koyarwa.

Sai dai kuma ana ganin idan har Buhari zai iya samun wannan nasara, to fa tilas idan ya ci sai ya hada kai da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi, domin su ne ke da makarantun firamare.

Sakandaren da ke karkashin gwamnatin tarayya ko alama ba su kai yawan makarantun firamare ba.

Haka nan kuma, idan za a iya tunawa, a lokacin kamfen na 2015, a cikin kudirorin ta, jam’iyyar APC a karkashin dan takarar ta Muhammadu Buhari, akwai alkawarin da ta yi a cikin rubutaccen daftarin cewa idan ta ci zabe a 2015, to za ta fi ilahirin dukkan makarantun sakandaren da ke jihohin Arewa maso Gabas inda ake fama da Boko Haram, ta katange su, kuma ta saka musu kamara mai hanyen masu shiga da fita, wato CCTV.

Sai dai kuma ga shi har APC ta kusa cika shekaru hudu a kan mulki, amma ko tayar da waccan maganar ma ba a kara yi ba.

A wurin kaddamarwar, Buhari ya ce har yanzu akwai sauran aiki a fannin yaki da cin hanci da rashawa, duk kuwa da cewa gwamnatin sa ta yi rawar gani wajen dakile manyan hanyoyi da dama inda ake wawurar kudade.

Ya ce ya na kokarin ganin ya cika dukkan alkawurran da ya dauka a lokacin zaben 2015.

Ya yi magana kan matsalar tsaro da kuma batun tattalin arziki.

Share.

game da Author