2019: Baka hada Haske da Duhu a ko-ina, Buhari Haske ne, Inji Oshiomhole

0

Shugaban jam’iyyar APC, Adam Oshiomhole ya bayyana cewa tattaunawar su da shugaban kasa Muhammadu Buhari tattaunawa ce don ci gaban jam’iyya da shirin fara kamfen da ake ciki, ba kamar yadda wasu ke ta yayadawa wai ganawar ta tuhuma ce ba.

Wasu da dama daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar APC sun zargi Oshiomhole da karbar cin hanci daga hannun wasu ‘yan takara a lokacin zaben fidda gwani na jihar.

Da dama sun zarge shi da karbar cin hancin har dala miliyan 80 daga wajen ‘yan takara a wancan lokaci.

Oshiomhole ya ce wannan zancen kanzon kurege ne, kuma jam’iyyar a shirye take ta tunkari zaben 2019.

” Buhari ba abin hada shi da wani dan takara bane. Babu inda zaka iya hada haske da duhu. Za mu tunatar wa mutane ayyukan da muka yi kuma zamu tabbata mun tallata dan takarar mu a ko-ina- a kasar nan.

Share.

game da Author