2019: Atiku zai fara Kamfen ranar Litini amma a shafin yanar gizo na Facebook

0

Kwamitin kamfen din dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar ya bayyana cewa za su fara kamfen gadan-gadan daga ranar litini.

Kwamitin ya bayyana cewa za fara ne ta hanyar sanar wa ‘yan Najeriya irin shirye shiryen da Atiku yayi wa kasa Najeriya idan yayi nasara a zabe 2019 ta shafin sa na sada zumunta na Facebook.

” Shirin gwamnatin mu idan muka kafa shine maida hankali wajen inganta rayukan mutanen kasar nan, samar da tsaro, ayyukan yi da ilmi da dai sauran su.

” Mun zabi mu fara ta shafin yanar gizo ne saboda mu iya isar da sakon mu ga kowa da kowa ganin cewa dama ci gaban da aka samu na haka ya samo asali ne tun a zaman mulkin PDP a baya, daga 1999 zuwa 2007.

Za a dai fara kamfen din shugaban kasa da na majalisar kasa daga ranar 18 ga watan Nuwamba, inda gwamnoni za su fara na su ne daga 1 ga watan Disamba.

Share.

game da Author