2019: Atiku ya kusa karbar takardar shiga Amurka – Gbenga Daniel

0

Babban Daraktan Kamfen na yakin neman aben Atiku Abubakar, Gbenga Daniel, ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC, Atiku Abubakar zai iya samun bizar shiga Amurka, idan ya nema a yanzu haka.

Daniel ya bayyana haka a cikin wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talbijin na Channels a jiya Laraba.

A can baya an rika yada jita-jitar cewa an hana Atiku shiga Amurka, zargin da shi kuma ya rika karyatawa.

Sai dai kuma ya ce ya nemi a ba shi bizar iznin shiga, amma bai samu ba, dalilin rashin zuwan sa kenan.

Daniel ya ce “Zan iya tabbatar muku da cewa a cikin ‘yan kwanakin da suka shude akwai umarni daga jami’an Amurka cewa Atiku zai iya zuwa ya karbi bizar iznin shiga kasar.”

A lokacin tattaunawar, Daniel ya kara da cewa zuguguta batun wawurar kudade da ake yi wa Atiku a shekaru da yawa da suka gabata zuwa yanzu, duk mummunar fahimta ce kawai.

Ya ce matsalar Najeriya ita ce, duk wani mummunan abu da aka dangata da shugabanni, sai a yi saurin amincewa ko gaskatawa.

Ya kuma ce idan ka dubi rahotannin da wasu jaridu suka buga a makonnin baya, za ka ga cewa Amurka ta ce ita ba ta da wata matsala da Atiku.

Share.

game da Author