ZARGIN ZAMBA: Kotu ta tsare mataimakin shugaban ma’aikatan Saraki a kurkuku

0

Babbar Kotun Tarayya ta bada umarnin a tsare Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki kurkuku.

An tsare Gbenga Makanjuala ne tare da wani mai suna Obiorah Amobi yau Laraba, bayan da aka fara tuhumar su da laifin yin zambar kudaden da suka kai naira bilyan 3.5.

An gurfanar da Makanjuala da Amobi ne tare da kamfanin Melrose General Services, Ltd, ana tuhumar su da aikta laifuka 11, a gaban Mai Shari’a Babs Kuewumi.

Mutumi na uku da ake tuhumar su tare, shi ne Kolawole Shittu, wani Jami’in kula da hada-hadar kudade, a ofishin Saraki.

Mai gabatar da kara daga ofishin EFCC, Ekene Iheancho, ya shaida wa kotun cewa wani Robert Mbonu, da yanzu ya cika wndon sa da iska, shi ne ya hada kai suka karkatar da naira bilyan 3.5 zuwa cikin asusun ajiyar kamfanin Melrose.

Share.

game da Author