A yau Alhamis ne Babbar Kotun Tarayya da ke Kano, ta a kara dage sauraren karar da aka gurfanar da tsohon gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau.
An gufanar da Shekarau ne ana tuhumar sa da salwantar naira miliyan 900 a hannun sa.
EFCC ce ta gurfanar da shi tare da tsohon ministan harkokin kasashen waje, Aminu Wali da wani mai suna Mansur Ahmed, inda ake tuhumar su da salwantar naira milyan 950.
Yayin da aka kirar karar a yau, Mai Shari’a Lewis Allagoa, wanda a yanzu ya kama aiki a kotun, y adage shari’a zuwa ranar 19, 20,da 21 Ga Nuwamba.
Mai Shari’ar ya maye gurbi Zainab Bage, wadda aka yi wa canjin wurin aiki.
Mai gabatar da kara daga EFCC, Johnson Ojogbane, tun da farko ya shaida wa kotu cewa su ukun da ake kara din sun hada baki sun karbi kudaden kai tsaye, wuri-naa-gugar-wuri, a ranakun 26 da 27 Ga Maris, ba tare da an bi ta ka’idar karbar kudi a banki ba.
Ya ce tsohuwar ministar harkokin man fetur, Deizani Maduekwe ce ta basu kudaden.
Discussion about this post